Mark 8

Yesu Ya Ciyar da Dubu Huɗu

1A kwanakin nan wani taro mai girma ya taru. Tun da yake ba su da abin da za su ci, sai Yesu ya kira almajiransa, ya ce, 2“Ina jin tausayin mutanen nan, kwanansu uku ke nan tare da ni, kuma ba su da abin da za su ci. 3In na sallame su gida da yunwa, za su kāsa a hanya, don waɗansu daga cikinsu sun zo daga nesa.”

4Almajiransa suka amsa suka ce, “Amma a ina, a wannan wurin da ba kowa, wani zai iya samun isashen burodi, don a ciyar da su?”

5Sai Yesu ya yi tambaya, ya ce, “Burodi guda nawa kuke da su?” Suka ce, “Bakwai.”

6Sai ya gaya wa taron su zazzauna a ƙasa. Bayan ya ɗauki burodin nan bakwai, ya yi godiya, sai ya kakkarya, ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutanen, suka kuwa yi haka. 7Suna kuma da ƙananan kifi kaɗan, ya ba da godiya dominsu, ya kuma ce wa almajiran su rarraba musu. 8Mutanen suka ci, suka ƙoshi. Daga baya, almajiran suka tattara gutsattsarin da suka rage cike da kwanduna bakwai. 9Wajen maza dubu huɗu ne suka kasance. Da ya sallame su, 10sai ya shiga jirgin ruwa tare da almajiransa, suka tafi yankin Dalmanuta.

11Farisiyawa suka zo suka fara yin wa Yesu tambayoyi. Don su gwada shi, sai suka nemi yǎ nuna musu wata alama daga sama. 12Sai ya ja numfashi mai zurfi, ya ce, “Don me wannan zamani yake neman ganin abin banmamaki? Gaskiya nake gaya muku, ba wata alamar da za a ba su.” 13Sai ya bar su, ya koma cikin jirgin ruwan, suka ƙetare zuwa ɗaya hayin.

Yistin Farisiyawa da na Hiridus

14Almajiran suka manta su riƙe burodi, sai dai guda ɗaya da suke da shi a cikin jirgin ruwan. 15Yesu ya gargaɗe su, ya ce, “Ku yi hankali, ku kuma lura da yistin Farisiyawa da na Hiridus.”

16Suka tattauna wannan da juna, suna cewa, “Don ba mu da burodi ne.”

17Da ya gane abin da suke tattaunawa, sai Yesu ya tambaye su, ya ce, “Don me kuke zancen rashin burodi? Har yanzu ba ku gane ko fahimta ba? Zukatanku sun taurare ne? 18Kuna da idanu, amma kun kāsa gani, kuna da kunnuwa, amma kun kāsa ji? Ba ku tuna ba? 19Da na kakkarya burodi guda biyar wa mutane dubu biyar, kwanduna nawa kuka kwashe cike da gutsattsarin?”

Suka amsa, “Sha biyu.”

20“Da na kuma kakkarya burodin nan bakwai wa mutum dubu huɗu, kwanduna nawa kuka kwashe cike da gutsattsarin?”

Suka ce, “Bakwai.”
21Ya ce musu, “Har yanzu ba ku fahimta ba?”

An Warkar da Makaho

22Suka iso Betsaida, sai waɗansu mutane suka kawo wani makaho, suka roƙi Yesu yǎ taɓa shi. 23Yesu ya kama hannun makahon ya kai shi bayan ƙauyen. Bayan ya tofa miyau a idanun mutumin, ya kuma ɗibiya masa hannuwansa, sai ya tambaye shi, ya ce, “Kana iya ganin wani abu?”

24Sai ya ɗaga kai, ya ce, “Ina ganin mutane, suna kama da itatuwa da suke tafiya.”

25Yesu ya sāke ɗibiya hannuwansa a idanun mutumin, sai idanunsa suka buɗe, ya sami gani, ya kuma ga kome sarai. 26Yesu ya sallame shi gida, ya ce, “Kada ka shiga cikin ƙauyen.
Waɗansu rubuce rubucen hannu suna da Kada ka faɗa wa kowa a ƙauyen


Shaidar Bitrus a kan Kiristi

27Yesu da almajiransa suka tafi ƙauyukan da suke kewaye da Kaisariya Filibbi. A hanya ya tambaye su, ya ce, “Wa, mutane suke ce da ni?”

28Suka amsa, suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yohanna Mai Baftisma, waɗansu Eliya, waɗansu kuma har wa yau sun ce, ɗaya daga cikin annabawa.” 29Sai ya yi tambaya, ya ce, “Amma ku fa, wa kuke ce da ni?”

Bitrus ya amsa, ya ce, “Kai ne Kiristi.
Ko kuwa Almasihu. “Kiristi” (da Girik) “Almasihu” kuma (da Ibraniyanci) duk suna nufin “Shafaffen nan.”

30Yesu ya gargaɗe su kada su gaya wa kowa kome a kansa.

Yesu Ya Yi Zancen Mutuwarsa

31Sai ya fara koya musu cewa, dole Ɗan Mutum yǎ sha wahaloli da yawa, dattawa, manyan firistoci da malaman dokoki kuma su ƙi shi. Dole kuma a kashe shi, bayan kwana uku kuma, yǎ tashi. 32Ya yi wannan zance a sarari. Sai Bitrus ya jawo shi gefe, ya fara tsauta masa. 33Amma da Yesu ya juya ya dubi almajiransa, sai ya tsauta wa Bitrus, ya ce, “Tashi daga nan Shaiɗan! Ba ka da alʼamuran Allah a zuciyarka, sai na mutane.”

34Sai ya kira taron wurinsa tare da almajiransa, ya ce, “Duk wanda zai bi ni, dole yǎ ƙi kansa, yǎ ɗauki gicciyensa yǎ bi ni. 35Domin duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, da kuma bishara, zai same shi. 36Me mutum zai amfana, in ya ribato duniya duka a bakin ransa? 37Ko kuma, me mutum zai bayar a musayar ransa? 38Duk wanda ya ji kunyata, da na kalmomina a wannan zamani na fasikanci da zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa lokacin da ya shiga cikin ɗaukakar Ubansa, tare da tsarkakan malaʼiku.”

Copyright information for HauSRK